Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shekaru arba'in da biyu da suka gabata a ranar 4 ga watan Nuwamba, daliban Iran suka kusa a ofishin jakadancin Amurka a Tehran, kasa da shekara guda bayan cimma nasarar juyin juya halin Musulunci wanda ya kawo karshen mulkin kama-karya na sarki Shah Pahlavi da Amurka ke marawa baya a shekarar 1979.
Daga nan ne aka sanya wa bikin ranar yaki da girman kan duniya ta kasa.
Ranar 4 ga watan Nuwamba kuma ita ce ranar dalibai ta kasa.
A kowace shekara, masu jerin gwanon a Tehran suna taruwa a wajen tsohon ofishin jakadancin Amurka, suna rera taken la’antar Amurka da Isra’ila.
Baya ga hakan kuma ranar 4 ga watan Nuwamba, tana tuna ranar da mirigayi Imam Khumaini wanda ya assasa jamhuriyar musulinci ya yi hijira zuwa Turkiyya, a 1964.
Hyaka kuma a irin ranar ce sojojin sarki Shah suka aikata kisan kiyashi wa dalibai da dama yayin wata zanga-zangar a ranar 4 ga Nuwamba, 1978.
342/